Shugaban majalisar kasashen turai, Donald Tusk, ya ce taron ya amince da ya mayar da wasu 'yan ciranin zuwa kasashensu na asali a inda wasu kuma za a ba su mafaka.
Taron ya kuma amince da yin karo-karon Yuro miliyan 120 domin daukar matakan hana kwararar 'yan cirani zuwa yankin turan.
Sannan Birtaniya tayi alkawarin jiragen ruwa da jirage masu saukar ungulu, a inda kasashen Jamus da Faransa da Belgium dukkanninsu suka yi alkawarin jiragen ruwa, domin yin sintiri a tekun. ABNA